
Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abba Yusuf, ta sanar da shirin raba kayan makaranta kyauta ga dalibai 789,000 a makarantu 7,092 a fadin jihar. Wannan mataki na nufin ƙarfafa karatun yara da rage yawan yaran da basa zuwa makaranta, musamman ga iyayen da ke fuskantar matsalar karancin kudi.
Kwamishinan watsa labarai na jihar, Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa wannan tsari yana daga cikin kudirin Gwamna Abba na inganta ilimi a Kano. Ya kuma jaddada cewa shirin zai ba wa yara damar samun ilimi mai nagarta, tare da taimaka wa iyayen da ba su da hali wajen biyan kuɗin kayan makaranta.
Wannan rabo zai fara ne a yau Litinin, inda Gwamna Abba zai jagoranci rabon a dakin taro na Coronation Hall. Ibrahim Waiya ya bayyana cewa wannan mataki yana daga cikin hanyoyin da gwamnatin ke bi don inganta ilimi a jihar.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa za a gina sabbin makarantun firamare a jihar a cikin wani shiri na inganta tsarin ilimi, tare da kashe kudi mai yawa wajen gyaran makarantun da ake da su.