
Jam’iyyar PDP ta bayyana shirin ta na gyara kurakuren da ta yi a zaɓen 2023, domin ta sake karɓe mulki daga hannun APC a shekarar 2027. Babban Sakataren PDP na Ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, ya bayyana cewa jam’iyyar ta shirya tsaf domin kalubalantar APC.
Anyanwu ya tabbatar da cewa babu wata baraka a cikin jam’iyyar, yana mai cewa PDP na kan hanya domin samun nasara a gaba. Ya kuma jaddada cewa jam’iyyar ta koyi darussa daga zaben 2023 da kuma cewa yanzu suna aiwatar da shirye-shiryen da zasu sa su zama babbar jam’iyyar siyasa a ƙasar.
Sanata Anyanwu ya yi magana kan hukuncin kotu da ya shafi matsayin sa a PDP, yana mai cewa har yanzu shi ne sakataren ƙasa. Ya bayyana cewa hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara bai kawar da shi daga mukamin sa ba, kuma zai ci gaba da rike shi har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukuncin ƙarshe.
A cikin jawabin sa, Anyanwu ya musanta zargin cewa akwai tsagi a cikin PDP, yana mai cewa jam’iyyar na ƙarƙashin cikakken shugabancin Umar Damagum. Ya ce PDP tana nan a tsaye kuma tana ci gaba da aiki tukuru domin dawo da martabar jam’iyyar.
PDP ta yi kira ga mabiyanta a Najeriya su ci gaba da bayar da goyon baya, tana mai tabbatar da cewa za ta sake farfaɗowa domin jan ragamar mulkin ƙasa a 2027.