Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Wike Ya Caccaki Solomon Dalung Kan Rashin Ayyuka a Gwamnatin Buhari

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana rashin jin dadinsa ga tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, wanda ya yi aiki a gwamnatin Muhammadu Buhari. Wike ya zargi Dalung da rashin kwarewa da kuma yin watsi da ayyukan ci gaban da gwamnatin Tinubu ke yi.

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Lere Olayinka, ya fitar, Wike ya ce Dalung bai taɓuka komai ba a lokacin da yake minista, wanda hakan ya sa ya kasa ganin alfanun gina hanyoyi da sauran ayyukan da suke faruwa a yanzu. Ya kara da cewa, Dalung na da ƙiyayya da shi da gwamnatin Tinubu, wanda hakan ya sa ya makance daga amsar gaskiya.

Wike ya jaddada cewa, “Dalung, wanda a lokacin yana a matsayin ministan matasa da wasanni, bai taɓuka komai ba, har ya kai ga cewa gina tituna ba ci gaba ba ne.” Ya kuma bayyana cewa, tun lokacin da Dalung yake minista, Najeriya ba ta taba samun nasarar shiga gasar cin kofin Nahiyar Afrika ba.

Ministan ya bayyana cewa tunani irin na Dalung yana nuni da rashin fahimta game da ci gaban da ake yi a fannin gine-gine da sauran ayyuka, yana mai jaddada cewa gina hanyoyi yana da matukar mahimmanci ga al’umma. Wannan caccakar ta jawo hankalin mutane da dama, inda wasu suka bayyana goyon bayansu ga Wike a kan wannan batu.