Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Shugaban PDP Ya Aike da Sabon Gargadi Kan Rikicin Jam’iyyar

Muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Iliya Damagum, ya yi gargadi kan rikicin da jam’iyyar ke fama da shi, inda ya bukaci mambobin jam’iyyar da su guji yada labaran ƙarya a kafafen sada zumunta. Ya jaddada cewa wannan yana iya kawo cikas ga haɗin kan jam’iyyar.

Damagum ya bayyana hakan ne a ƙarshen taron kwanaki biyu kan wayar da kai a fannin yaɗa labarai, wanda aka gudanar a Birnin Kebbi. Ya ce, “Jam’iyyar PDP ta fi ƙarfin kowane mutum, kuma rikice-rikicen cikin gida ba za su iya kawo ƙarshenta ba.”

Ya yi kira ga shugabanni da mambobin jam’iyyar da su mayar da hankali kan haɗin kai maimakon rarrabuwar kawuna. Umar Damagum ya tabbatar da cewa yana da niyyar tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a cikin jam’iyyar, yana mai cewa ba za a lamunci rashin adalci ko yaɗa farfaganda a ƙarƙashinsa ba.

Shugaban jam’iyyar ya kuma yi gargadi kan illar rura wutar rikici da fifita son kai a kan haɗin kan jam’iyya, yana mai cewa hakan zai iya shafar abubuwan da shugabannin jam’iyyar suka gina a kai. Ya ƙara da cewa PDP za ta ci gaba da zama da ƙarfinta, tare da yin kira ga dukkan mambobin da su fifita muradun jam’iyya a kan bukatun kansu domin tabbatar da ci gabanta.