
Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji, Hon. AbdulMumin Jibrin Kofa, ya bayyana cewa jam’iyyar APC a jihar Kano ba za ta yi tasiri a zaben 2027 ba. Kofa, wanda ke cikin jam’iyyar NNPP, ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake tattaunawa game da rikice-rikicen da ke faruwa a cikin APC.
A cewar Kofa, shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, zai fitar da dan takara, amma hakan ba zai kawo canji mai kyau ba, ganin cewa akwai rigingimu da suka hana jam’iyyar ci gaba. Ya zargi wasu daga cikin manyan APC da hada hannu wajen rashin nasarar takarar dan gidan Ganduje a zaben 2023.
Hon. Kofa ya bayyana cewa adawa da tafiyar Kwankwasiyya na daga cikin abubuwan da ke haifar da cakwakiya a siyasar Kano. Ya ce idan ana so jam’iyyar ta yi nasara, dole ne a magance wadannan matsaloli da ke ciki.
Ya kara da cewa, “Ganduje ne zai fitar masu da dan takara, duk da dai zamu ka da dan takarar ko ya fitar.” Kofa ya yi zargin cewa, rigingimun APC a Kano sun ki karewa ne saboda adawa da ake yi da Rabi’u Musa Kwankwaso da gwamnan jihar.
Daga karshe, ya jaddada cewa har yanzu akwai manyan kalubale da jam’iyyar ke fuskanta, wanda idan ba a magance su ba, to zabe mai zuwa na 2027 zai zama kalubale ga APC a Kano.