
Ƴan ta’addan Boko Haram sun kai hari mai ƙarfi a sansanin sojoji a jihar Borno, wanda hakan ya haifar da asarar rayuka da yawa daga cikin jami’an tsaro. A lokacin harin da aka kai a ƙaramar hukumar Damboa, adadin sojojin da suka rasa rayukansu na ci gaba da ƙaruwa kwanaki hudu bayan faruwar lamarin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:00 na yamma a sansanin FOB na rundunar 25TF Brigade. Majiyoyi daga rundunar sojoji sun bayyana cewa tawagar bincike na ci gaba da gano gawarwakin jami’an tsaron da suka rasa ransu.
A halin yanzu, hukumomin soji a Maiduguri da Abuja ba su fitar da wata sanarwa dangane da harin ba. Amma, a cewar majiyoyi, an gano gawarwaki fiye da 12, yayin da wasu sojoji da ƴan sa-kai har yanzu ba a gano inda suke ba.
Kodayake an turo ƙarin jami’ai daga babban sansanin, har yanzu ana fama da kalubale daga bama-baman da ƴan ta’addan suka dasa. Wannan harin ya jawo hankalin al’umma kan yadda Boko Haram ke ci gaba da zama barazana ga tsaro a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya.