
Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta ya musanta jita-jitar cewa yana shirin sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. A cewar gwamnan, wannan labari maras tushe yana fitowa ne daga makiyansa da ke son kawo rudani a cikin jam’iyyar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sir Festus Ahon, ya fitar, ya ce gwamnan yana cikin jam’iyyar PDP daram kuma ba zai sauya sheka ba. Ya bayyana cewa gwamnan na samun karbuwa daga al’ummar jihar Delta, wanda hakan ya tabbatar da cewa babu dalilin da zai sa shi barin PDP.
Jita-jitar ta biyo bayan zarginsu na APC da gwamnan da gazawa wajen inganta ababen more rayuwa a jihar, duk da yawan kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya. Gwamna Oborevwori ya yi watsi da wannan zargi, yana mai cewa zai ci gaba da kyautata wa al’ummar jiharsa.
Sir Festus ya roki jama’a da su yi watsi da jita-jitar, yana mai tabbatar da cewa gwamnan zai ci gaba da aiki tare da gwamnatin tarayya domin amfanin jihar Delta da al’ummar Najeriya baki ɗaya.
Wannan musantawa ta zo ne a lokacin da wasu ‘yan siyasa ke nuna damuwa game da karfin gwamnan da kuma hadin kan da yake samu daga al’umma, wanda hakan ke janyo hankalin ‘yan adawa. Gwamnan ya nanata cewa yana mai da hankali kan cika alkawuran da ya yi wa al’ummar jihar a lokacin yakin neman zabe.