
A jihar Edo, rikicin siyasa ya kara tsananta yayin da ‘yan majalisar kansiloli suka tsige shugabannin kananan hukumomi guda biyu. Shugabannin da aka tsige sun hada da Dr. Kelly Ehidiamen Inedegbor na karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas da Tajudeen Alade na karamar hukumar Akoko-Ado.
Majalisar ta bayyana cewa tsigewar ta biyo bayan zargin rashin ɗa’a da karya dokar rantsuwa. Duk da hakan, shugabannin da aka tsige sun ce matakin ba zai yi tasiri ba, suna mai cewa an sabawa tanadin doka.
Bayan tsigewar, an sanar da dakatar da wasu kansiloli uku saboda dalilai da ba a bayyana ba. A yayin taron da aka gudanar a hedkwatar karamar hukumar Akoko-Edo, an bayyana cewa sabon shugaban kansiloli ya karbi ragamar shugabanci tare da kafa kwamitin da zai dawo da kadarorin gwamnati da suka bata.
Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Rt. Hon Kabiru Adjoto, ya nuna gamsuwarsa da yadda aka gudanar da tsigewar cikin lumana. Shugaban karamar hukumar Akoko-Ado, Tajudeen Alade, ya zargi masu tsige shi da kulla masa makirci domin su wawure dukiyar al’umma.