Ana Shirin Kafa Sabuwar Jam’iyya a Najeriya

kungiyar League of Northern Democrats (LND) karkashin jagorancin Sanata Ibrahim Shekarau ta bayyana shirin kafa sabuwar jam’iyya domin buga zabe a shekarar 2027. Wannan mataki na zuwa ne bayan zarginsu cewa jam’iyyun APC da PDP sun gaza wajen cika burin ‘yan Najeriya.

LND ta yi kira ga hadin gwiwa da kungiyoyin siyasa daga Kudu domin kafa jam’iyyar mai karfi. Jagoran kungiyar, Dakta Umar Ardo, ya bayyana cewa wannan shirin yana da alaka da bukatar ‘yan Najeriya na canji daga mulkin da ba ya cika musu burinsu.

A martanin da jam’iyyar APC ta fitar, ta ce shirin LND ba zai zama barazana ga nasararta a zaben 2027 ba. Alhaji Bala Ibrahim, Daraktan Yada Labaran APC, ya jaddada cewa manufofin jam’iyyar suna haifar da sakamako mai kyau.

Kungiyar LND ta yi kira ga ‘yan Najeriya su marawa wannan yunkuri baya domin samun canji a tsarin mulkin kasar. Wannan tattaunawa na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara magana kan shirye-shiryen zaben 2027, inda jam’iyyun siyasa ke neman goyon bayan ‘yan kasa.