
Shugaban hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana kwarin gwiwar cewa sojojin Najeriya za su ga karshen ‘yan ta’addan da suka addabi kasar. Ya bayyana wannan a yayin ziyarar da ya kai wa dakarun soji a karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau.
Janar Musa ya jaddada cewa, a wannan shekarar, babu wata kafa da ‘yan ta’adda za su samu don gudanar da ayyukansu. Ya tabbatar da cewa gwamnatin Najeriya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da ta’addanci, tare da tabbatar da cewa dakarun sojin sun samu kayan aikin da suka dace don cimma wannan buri.
Ya yi kira ga sabbin manyan jami’an da aka kara wa girma su dauki matakan da suka dace don kakkabe ‘yan ta’adda da masu satar man fetur. Janar Musa ya ce lokaci ya yi da za a kawo karshen matsalar da ta addabi kasar fiye da shekaru goma sha biyar.
Har ila yau, ya gargadi al’ummar Najeriya da su guji hulda da ‘yan ta’adda, yana mai cewa hakan na kara dagula lamarin tsaro. Ya yi wannan kira ne a matsayin wani mataki na rage karfin ‘yan ta’adda da tabbatar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.
Janar Musa ya bayyana cewa shekarar 2025 za ta zama shekara mai muhimmanci wajen kawo karshen ta’addanci a Najeriya, yana mai kira ga dakarun soji da al’ummar kasa su hada kai wajen cimma wannan buri. Wannan furuci na shugaban soji na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar manyan kalubale na tsaro, musamman a jihohin arewa.