
Yan ta’addan ƙungiyar Lakurawa sun kai harin ta’addanci a ƙaramar hukumar Argungu a jihar Kebbi, inda suka kashe jami’an ƴan sanda guda biyu. Harin ya faru ne a yayin da jami’an ƴan sandan ke gudanar da bincike a shingen tsaro lokacin da ƴan ta’addan, masu yawa fiye da 50, suka kai wa shingen hari daga kan babura.
Bayan kashe jami’an, ƴan ta’addan sun sace shanu sama da 200 daga ƙauyen Natsini, wanda hakan ya jawo fargaba a tsakanin mazauna yankin. Wani mazauni, Abubakar Augie, ya bayyana cewa shanun da aka sace na wani fitaccen ma’aikacin gwamnati ne mai suna Lawali Black.
Shugaban karamar hukumar Argungu, Aliyu Gulma, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce majalisar ƙaramar hukumar ta gudanar da taron tsaro don tattauna matakan da za a dauka. Gwamnatin jihar ta umarci jami’an tsaro da su bi sahun ƴan ta’addan domin ƙwato shanun da aka sace.
Har yanzu, ba a samu jin ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kebbi ba. Wannan lamari na ƙara jaddada bukatar karin tsaro a jihar, wanda gwamnan jihar, Nasir Idris, ya tabbatar da cewa babu sansanin ƴan bindiga a Kebbi, amma suna shigowa daga jihohin makwabta.