
Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), a gidansa a Minna, babban birnin jihar Neja. Ziyarar ta kasance mai muhimmanci wajen karfafa alaka da tattauna shawarwari kan matsalolin da Najeriya ke fuskanta.
Obi ya bayyana cewa ziyarar ta kasance bisa manufar gina kasa da hadin kan al’umma. A yayin tattaunawar, ya jaddada cewa akwai bukatar a samar da sabuwar Najeriya, wacce zai yiwu idan aka yi aiki tare da dukkanin bangarorin al’umma.
Ya yaba wa Janar Babangida bisa basirarsa da fahimtarsa, yana mai cewa: “Basirar Janar Babangida da fahimtarsa suna da matukar muhimmanci. Ina matukar godiya da damar da nake samu na ziyartarsa domin jin shawarwarinsa masu cike da hikima.”
Obi ya kuma ziyarci tsohon gwamnan jihar Neja, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu, inda suka tattauna kan muhimmiyar aikin gina kasa da hakkin al’umma wajen samar da kyakkyawar makoma ga Najeriya. Ya bayyana cewa hadin kai na da matukar muhimmanci wajen cimma wannan buri.
Wannan ziyara ta Obi ta zo ne a lokacin da ake ci gaba da tattauna kan hanyoyin da za a inganta tattalin arziki da kyautata rayuwar al’umma a Najeriya.