‘Tabarbarewar Dangantaka’: Masana Sun Hango Illar Rashin Nada Jakadun Najeriya

Shekara guda da wata ɗaya kenan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dawo da jakadun Najeriya gida, kuma har yanzu bai naɗa sababbi ba.

Tun bayan dawo da su ranar 2 ga Satumba, 2023, ofisoshin jakadancin Najeriya 109 a kasashen waje sun kasance babu cikakken wakilci na jakadanci.

Masana harkokin diflomasiyya da tsofaffin jakadu sun ce rashin jakadu na rage tasirin dangantakar Najeriya da sauran kasashe.

Sun bayyana cewa masu kula da ofisoshin yanzu ba su da matsayin da ya dace don ganawa da ministocin harkokin waje na kasashen da suke ciki.

A matsayinsu na daraktoci a ma’aikatar gwamnati, suna fuskantar iyakoki wajen gudanar da ayyukan da ke buƙatar amfani da ikon jakadu.

Jakada Suleiman Dahiru ya caccaki jinkirin, yana mai cewa ya kamata a nada sababbin jakadu kafin a kira tsofaffin gida.

Ya yi gargadin cewa jinkirin zai iya hana a nada wasu jami’an diflomasiyya da suka cancanta saboda shekarunsu ya kusa kai na ritaya.

Wani tsohon jakada ya ce wasu ƙasashe na iya ƙin hulɗa da ƙananan jami’ai, abin da zai ƙara tsananta dangantakar Najeriya da su.

Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan yarjeniyoyi da dama na ƙasa da ƙasa, amma ana buƙatar jakadu domin tabbatar da cewa Najeriya ta ci moriyarsu.

Ministan harkokin waje, Yusuf Tuggar ya tabbatar wa da ’yan Najeriya cewa, duk da ƙalubalen, gwamnati na aiki kan matsalar kuma za ta warware ta nan gaba.

A halin yanzu, ana ci gaba da jiran nadin sababbin jakadun Najeriya.

Muna kira ga gwamnati da ta gaggauta magance wannan matsala, domin tabbatar da cewa Najeriya na da cikakken wakilci a kasashen waje.

Hakan zai taimaka wajen inganta dangantakar Najeriya da sauran kasashe, da kuma kare muradun kasar a duniya.