Rikici Ya ɓarke a Jihar Neja Tsakanin Ƴan Banga da Mazauna Unguwa

An samu tashin hankali a birnin Minna na jihar Neja, inda rikici ya ɓarke tsakanin Ƴan banga da mutanen unguwa. Wannan rikici ya faru ne lokacin da Ƴan bangan suka kai farmaki ga wasu wuraren da ake zargin maɓoyar masu aikata laifuka ne.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da cewa an kwantar da mutum biyu, waɗanda suka samu raunuka a asibiti sakamakon wannan rikici. Mazauna unguwar Soje sun yi gumurzu da Ƴan banga, suna mai bayyana cewa wuraren da aka kai farmakin ba su cikin jerin wuraren da Ƴan daba ke samun mafaka.

Rikicin ya faru ne a ranar Talata da daddare, kuma an bayyana cewa ɗaya daga cikin Ƴan bangan ya samu rauni a lokacin arangamar. SP Abiodun ya ce an umurci Ƴan banga su riƙa aiki tare da Ƴan sanda idan za su kai farmaki kan duk wani wurin da ake zargin akwai masu aikata laifuka.

A halin yanzu, jami’an tsaro na cigaba da bincike kan wannan lamari, tare da ƙoƙarin cafke waɗanda ake zargin da suka tsere. Al’umma na fatan samun zaman lafiya a yankin bayan wannan rikici.