
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Malam Nuhu Ribadu, mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan harkokin tsaro, ya bayyana hanyoyin da za a bi domin dakile matsalar tsaro a Najeriya. Ribadu ya jaddada cewa nasarar yaki da ta’addanci da sauran laifuka ba za ta yiwu ba sai da hadin gwiwar al’umma da hukumomin tsaro.
Ribadu ya bayyana cewa, yana da matukar muhimmanci kowane mutum ya bayar da rahoto kan duk wani abu da ya shafi tsaro, domin taimakawa wajen dakile matsalolin tsaro. Ya ce, “Tsaro hakkin kowa ne, ina kira ga kowa da kowa ya gaggauta bayar da rahoto kan duk wani abu da ake zargi ga hukumomin tsaro.”
Ya kuma yabawa dakarun soji da ‘yan sanda bisa kokarinsu na samar da tsaro a shekarar da ta gabata, inda ya tabbatar da cewa a shekarar 2025, za a magance matsalolin tsaro ta hanyar hadin kai da dabaru na zamani.
Ribadu ya bayar da tabbacin cewa, tare da hadin kan sojoji da hukumomin tsaro, a cikin shekaru masu zuwa za a iya samun ingantaccen tsaro a Najeriya. Hakan na nuni da cewa gwamnatin tana sane da matsalolin da jama’a ke fuskanta, kuma tana daukan matakai masu inganci don samun daidaito a harkokin tsaro.