NLC Ta Bukaci Tinubu Ya Janye Kudirin Haraji Daga Gaban Majalisar Tarayya

Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta sake nanata kiranta ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya janye kudirin haraji da ke gaban Majalisar Tarayya. A cikin sakon barka da shiga sabuwar shekara, shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana cewa janye wannan kudiri yana da matukar muhimmanci domin kare walwala da jin dadin ma’aikatan Najeriya.

Ajaero ya yi kira ga dukkan gwamnatoci, daga matakin ƙasa har zuwa kananan hukumomi, da su aiwatar da dokar sabon mafi ƙarancin albashi. Ya ce, wannan mataki na janye kudirin haraji yana da muhimmanci don sake tattaunawa kan abubuwan da suka shafi talakawa da ma’aikata.

Shugaban NLC ya yi nuni da cewa cire tallafin man fetur bai haifar da wani ci gaba ba, har ma ya jefa al’umma cikin ƙunci da tsadar rayuwa. Haka zalika, ya bukaci gwamnati ta inganta alaka da ma’aikata ta hanyar tattaunawa da mutunta yarjejeniyoyin da aka kulla.

Joe Ajaero ya ce: “Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta janye kudirin harajin da ta gabatar a gaban Majalisar Dokoki domin sake zaman kansa da dukkan masu ruwa da tsaki.” Wannan kiran na NLC yana nuni da matsayin da kungiyar ke dauka kan inganta yanayin rayuwar ma’aikata a Najeriya, musamman a wannan lokacin da ake fuskantar matsalolin tattalin arziki.