
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya karyata ikirarin cewa ya yi barazana ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. A cikin sanarwar da aka fitar daga gidan gwamnatin jihar, gwamnan ya bayyana cewa ya yi gargadi ne kawai game da kudirin gyaran haraji domin tabbatar da adalci ga talakawa.
Gwamnatin Bauchi ta ce caccakar da aka yi wa Bala Mohammed na siyasa ne, saboda kasancewarsa dan jam’iyyar PDP. An bayyana cewa gargadin da ya yi ba ya nufin yin barazana ga gwamnatin tarayya, illa kawai domin ganin an dawo da adalci a cikin tsarin haraji.
Gwamnan ya yi nuni da cewa akwai gwamnonin APC da suka yi adawa da kudirin harajin, amma martani akan nashi ya bayyana alamar cewa ana neman bata masa suna ne a saboda jam’iyyar da yake wakilta.
Haka kuma, gwamnatin jihar ta zargi gwamnatin tarayya da rashin shawarwari kafin gabatar da kudirin harajin ga majalisar dokoki. Wannan yana nuni da rashin kulawa ga lamuran da zasu inganta rayuwar al’umma.