Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Akpabio Ya Bayyana Shirin APC Akan Jihohin Kudu Maso Kudu a 2027

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa jam’iyyar APC tana shirin lashe dukkan jihohin Kudu maso Kudu a zaɓen 2027. Akpabio ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Gwamna Monday Okpebholo a gidansa da ke Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

Akpabio ya nuna cewa APC tana da niyyar karɓar sauran jihohi huɗu da ba su ƙarƙashin ikonta a shiyyar Kudu maso Kudu. Ya jaddada cewa ya koma APC ne don jawo hankalin mutanen yankin zuwa jam’iyyar, tare da tabbatar musu da cewa za su samu wakilci mai kyau a matakin ƙasa.

Ya ce, “A gwamnatin APC, da yawa daga cikinmu sun yanke shawarar cewa akwai buƙatar mu sauya sheƙa, domin samun damar wakiltar jama’armu a matakin ƙasa.”

Akpabio ya kuma bayyana cewa akwai alamu masu kyau a game da nasarar APC a zaɓen 2027, inda ya yi nuni da cewa jam’iyyar tana da shirin kawo ƙarin jihohi a ƙarƙashin ikonta.