Ragin Farashin Fetur a Najeriya: Muhimman dalilai guda Hudu

Matatar Ɗangote da kamfanin mai na ƙasa, NNPCL, sun rage farashin litar man fetur daga sama da N1,000 zuwa N899 a makon da ya gabata. Wannan mataki ya jawo farin ciki a tsakanin ƴan Najeriya, musamman a lokacin da ake cikin yanayi na tsadar rayuwa.

Ga wasu muhimman dalilai da suka sa aka rage farashin fetur:

1. Yanayin Kasuwa: Gwamnatin tarayya ta saki tsarin ƙayyade farashin man fetur, wanda ya ba kasuwar damar da ta dace wajen tsara farashin. Alhaji Aliko Ɗangote ya bayyana cewa yanayin kasuwa ne ya sa farashin man ya sauka.

2. Faɗuwar Darajar ɗanyen Mai a Duniya: Farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya fadi zuwa $70 kan kowace ganga. Wannan faɗuwar ta taimaka wajen rage farashin fetur a Najeriya.

3. Farfaɗowar Naira: Naira ta fara farfaɗowa kan Dalar Amurka, wanda hakan ya rage farashin mai a kasuwa. A cikin ‘yan makonnin da suka gabata, Naira ta ragu daga N1,800 zuwa N1,500 kan kowace Dala.

4. Cinikin ɗanyen Mai da Naira: Fara hada-hadar ɗanyen mai a Naira tsakanin gwamnatin Najeriya da matatar Ɗangote ya taka muhimmiyar rawa wajen sauke farashin litar fetur. Wannan tsari ya taimaka wajen farfaɗo da tattalin arziki.

Wannan sauyin farashin ya yi tasiri mai kyau a kan rayuwar ƴan Najeriya, yana kuma ba da fata ga al’umma game da inganta yanayin kasuwanci a cikin ƙasar.