
Rundunar sojojin Operation Fansan Yamma ta musanta rahotannin da suka yi nuni da cewa an jefa bama-bamai kan fararen hula a jihar Sakkwato. A cikin wata sanarwa da Kodinetan sashen yaɗa labarai na rundunar, Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi, ya bayyana cewa jirgin yaƙin sojoji ya kai samame ne kan wasu da ake zargin suna da alaƙa da ƴan ta’addan Lakurawa.
Kanal Abubakar ya jaddada cewa sojojin ba su yi kuskure ba wajen jefa bam a kan fararen hula. Ya roki jama’a su rika dogaro da sahihan labarai, domin kaucewa yada rahotannin da za su iya tada hankula game da ayyukan sojoji. Wannan na zuwa ne bayan rahotannin da suka bayyana cewa an yi luguden wuta kan kauyuka biyu.
Ya bayyana cewa tattara bayanan sirri na da matuƙar muhimmanci a yaki da ƙungiyar ƴan ta’adda, wanda wannan ne zai tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin fararen hula. Hakanan, Kanal Abubakar ya yi kira ga jama’a da su yi taka tsan-tsan kan rahotannin da ba su tabbata ba, musamman game da yaki da ƴan ta’adda da masu aikata laifuffuka.
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa duk wani samame da aka yi, yana da tushe daga bayanan sirri da aka tattara, kuma an yi shi ne domin tabbatar da tsaron al’umma daga barazanar ƴan ta’adda. Wannan sanarwa ta fito ne a lokacin da ake ci gaba da fuskantar kalubale daga ƴan ta’adda a yankin Arewa maso Yamma.