“Ba Yan Ta’adda bane” Hukuma ya Fadi abun da yafi Hallaka Yan Ƙasa

Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) reshen jihar Kano, Umar Matazu, ya bayyana cewa yawaitar haɗurran mota a Najeriya na jawo asarar rayuka fiye da ayyukan ta’addanci da ƴan bindiga. Wannan bayani ya bayyana ne a lokacin da ya ziyarci sababbin shugabannin ƙungiyar ƴan jarida reshen jihar.

Umar Matazu ya nuna damuwa kan yawan haɗurran ababen hawa da ke faruwa a ƙasar, inda ya ce, “Yawan mace-macen da haɗurran mota ke jawo ya zarce na ta’addanci. Akwai lokuta da a wani hatsarin mota, asarar rayukan da ake samu na iya kaiwa sama da mutum 40.”

Ya ƙara da cewa, a cikin watanni biyu da suka gabata, yawan mace-macen da aka samu daga haɗurran mota ya fi na ƴan bindiga. Kwamandan ya yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a kan muhimmancin kiyaye dokokin tuƙi da bin ƙa’idojin zirga-zirga.

Matazu ya bayyana cewa, duk da yawan hare-haren da ƴan bindiga ke yi, haɗurran mota suna ci gaba da zama babban matsala ga lafiya da tsaro a Najeriya. Ya yi kira ga al’umma su kasance masu bin doka da oda a lokacin tuƙi domin rage haɗarin haɗurran mota.

A ƙarshe, ya jaddada cewa, inganta wayar da kan jama’a kan wannan batu yana da matuƙar muhimmanci wajen rage haɗurran mota da asarar rayuka a ƙasar.