
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da gagarumar nasara da ta samu a fagen yaki da laifuffuka a shekarar 2024. A cikin rahoton da Sufeto Janar, Kayode Egbetokun, ya fitar, an kama mutane 30,313 bisa zarge-zarge daban-daban, tare da kwato bindigogi 1,984 da harsashi 23,250.
A yayin taron tattaunawa da manyan jami’an ‘yan sanda a Abuja, Egbetokun ya yaba wa jami’an bisa jajircewar su wajen rage laifuka da kuma karfafa dangantaka tsakanin jama’a da ‘yan sanda. Ya bayyana cewa, a cikin wannan shekarar, an samu nasarar ceto mutane 1,581 daga hannun masu garkuwa da mutane a jihohi daban-daban.
Sufeto Janar ya shaida wa manema labarai cewa rundunar za ta mayar da hankali kan amfani da sabbin fasahohi da dabarun aiki don tunkarar kalubalen tsaro na shekarar 2025. Ya yi kira ga manyan jami’an su rungumi sababbin kayan aiki da tsare-tsaren zamani da za su inganta aikin tsaro.
A cikin makon da ya gabata, rundunar sojin Najeriya ta gudanar da nasarori kan ‘yan ta’adda a jihar Anambra, inda ta ritsa da wasu daga cikin ‘yan ta’addar da ke gudanar da ayyukan ta’addanci.
Wannan nasara ta ‘yan sanda ta karfafa gwiwar jama’a da hukumomi, tare da tabbatar da cewa za a yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da zaman lafiya, musamman a lokacin bukukuwan karshen shekara.