Gwamnan Katsina Ya Cika Alkawari, Malaman Makaranta Sun Yi Fari Ciki

Ma’aikatan jihar Katsina sun bayyana farin ciki da Gwamna Dikko Radda ya fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000. Wannan mataki ya biyo bayan alkawarin da gwamnan ya yi na aiwatar da dokar sabon albashin bayan tattaunawa da ƴan kwadago.

Wani malamin makaranta, Malam Bashir Yusuf, ya shaida wa manema labarai cewa wannan ƙarin albashi zai taimaka musu matuka a wannan lokacin da tsadar rayuwa ta karu. Ya bayyana cewa gwamnati ta biya albashin watan Disamba yau, inda suka samu ƙarin albashi kamar yadda gwamna ya yi alƙawari.

Hadimin gwamnan Katsina, Isah Miqdad, ya tabbatar da farawa biyan sabon albashin a shafin X, inda ya jaddada cewa gwamna ya cika alkawarin da ya ɗauka.

Malam Bashir ya yabawa gwamnatin Katsina bisa wannan mataki, yana mai cewa wannan zai rage raɗaɗin kuncin da ma’aikata ke fuskanta. Ya ce, “Kamar yadda Gwamna Dikko Radda ya yi alkawari, an fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi, kuma hakan ya kawo farin ciki ga ma’aikata.”

Gwamnan ya tabbatar da cewa sabon albashin zai kasance mai inganci ga ma’aikata a jihar, yana mai fatan cewa wannan mataki zai kawo ci gaba a fannin ilimi.