Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Zulum Ya Koka Kan Bukatar Gyaran Madatsar Ruwan Alau a Borno

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta gyara madatsar ruwan Alau, wanda ta ɓalle a wannan shekarar. Zulum ya bayyana cewa lokaci na tafe kafin damina, wanda zai iya haifar da mummunan ambaliya idan ba a dauki matakin gaggawa ba.

A yayin taron karɓar rahoto daga kwamitin da ya binciki musabbabin rugujewar madatsar, Zulum ya nuna damuwarsa game da illolin da ambaliyar ruwan ta yi wa garuruwan Maiduguri da Jere. Ya ce, “A mako mai zuwa za mu shiga watan Janairu, kuma damina zata dawo. Muna da ƙarancin lokaci don gyara wannan madatsar.”

Gwamnan ya yi nuni da cewa idan ba a fara aikin gyaran ba nan da ƴan kwanaki, zai tilasta masa kai wa ga shugaban ƙasa don roƙon gaggauta daukar mataki. Zulum ya ce, “Muna fatan tawagar gwamnatin tarayya ta ziyarci Maiduguri don tattaunawa da kwamitin da muka kafa kan wannan batu.”

Hakanan, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kyautata kulawa ga al’amuran da suka shafi lafiyar al’umma a jihar, yana mai cewa, “A matsayin gwamnatin jiha, za mu yi iya bakin ƙoƙarinmu domin ganin an dauki matakin da ya dace.”

Gwamna Zulum yana fatan cewa wannan roƙo zai jawo hankalin gwamnatin tarayya kan muhimmancin gyaran madatsar ruwan da zai kare al’ummar jihar daga ambaliyar ruwa a lokacin damina.