
Ma’aikatar Noma da Samar da Abinci ta gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani shiri na raba kayan aikin noma ga manoman alkama 6,000 a jihar Kano. Wannan shiri na nufin taimakawa manoma wajen inganta harkar noma da rage dogaro da kasashen ketare.
Kayayyakin da aka raba sun haɗa da taki da iri, inda gwamnati ta bayar da tallafin kashi 75% na kuɗin kayan. Wannan yana nufin cewa manoman za su biya kashi 25% na farashin kayan, wanda wannan ya sa kayan sun zama masu rahusa ga kowane manomi. Manomi zai karɓi buhunan taki uku da buhu ɗaya na irin alkama mai nauyin kilo 50.
Wakilin ministan noma, Isa Isyaku Hotoro, ya bayyana cewa manoman da za su amfana da wannan tallafi sun fito ne daga ƙananan hukumomin Bunkure, Ajingi, da Gaya. Haka zalika, gwamnatin tarayya ta ware filaye masu fadin hekta 3,000 a wurare na musamman guda 12 domin gudanar da noman.
Manoman sun nuna farin ciki bisa wannan tallafi, suna mai cewa hauhawar farashin taki da iri ya sa da dama sun rage yawan gonakin da suke nomawa. Sun roƙi gwamnatin da ta tabbatar da cewa ana raba kayan cikin lokaci domin su samu damar shiri tun da wuri.
Wannan shiri na gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na nufin inganta harkar noma a Najeriya, tare da tabbatar da cewa manoma sun samu kayan aiki da suka dace don samun nasara a cikin aikin su. Tallafin na da matukar tasiri wajen habaka noma da kuma rage dogaro da kayayyakin abinci daga kasashen waje.