Tinubu Ya Gabatar da Kasafin Kudin 2025 a Majalisar Tarayya

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudirin kasafin kuɗin shekarar 2025 a gaban Majalisar Tarayya. Wannan gabatarwa ta kasance mai matuƙar muhimmanci, inda shugaba Tinubu ya bayyana tsare-tsarensa na inganta tattalin arziki da samar da tsaro ga al’ummar Najeriya.

Tinubu ya isa majalisar tare da manyan jami’an gwamnati, ciki har da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, da Ministan Kudi, Wale Edun. A cikin jawabinsa, ya bayyana cewa kasafin kuɗin 2025 zai ƙunshi Naira tiriliyan 47.9, tare da manufofin da suka haɗa da inganta tsaro, gyara tattalin arziki, da rage talauci.

A yayin jawabin, Tinubu ya ce, “Manufar kasafin 2025 ita ce dawo da kwanciyar hankali, tare da cike gibin tattalin arzikinmu.” Ya kuma jaddada cewa gwamnatin sa na aiki tukuru wajen inganta yanayin kasuwanci da samar da ayyukan yi ga matasa.

Shugaban ya bayyana cewa, a cikin shekarar 2024, gwamnatin sa ta tara Naira tiriliyan 14.55 a matsayin kudaden shiga, wanda ya kai kashi 75 cikin 100 na hasashen da aka yi. Hakan ya nuna cewa gwamnatin na kan hanya madaidaiciya wajen inganta tattalin arziki.

Kasafin kuɗin ya kuma yi hasashen cewa hauhawar farashi zai ragu daga kashi 34.6% zuwa kashi 15% a 2025, yayin da darajar Naira za ta ƙaru daga N1,700 zuwa N1,500 a kowanne dala.

A ƙarshe, Tinubu ya bayyana cewa kasafin kuɗin 2025 yana da matuƙar mahimmanci wajen inganta makomar Najeriya, tare da fatan samun goyon bayan dukkan masu ruwa da tsaki a cikin al’umma.