Gwamna Radda Ya Kaddamar da Tallafin Naira Biliyan 3.9 ga Al’umma

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya sanar da shirin raba tallafin Naira biliyan 3.9 domin inganta rayuwar al’umma a jihar. Wannan tallafi zai tafi ne ga yankuna 65, manoma 19,068, da kananan ‘yan kasuwa 4,095.

Shirin Mai taken KT-CARES, wanda aka kaddamar a filin wasa na Malumfashi, na nufin tallafawa marasa galihu tare da bunkasa tattalin arziki. Gwamna Radda ya bayyana cewa tallafin zai ba da gudummawa wajen inganta harkokin kasuwanci da noma a jihar.

A karkashin wannan shirin, za a bai wa yankuna kudi daga Naira miliyan 2 zuwa miliyan 11 domin gudanar da ayyukan da suka zaba. Hakanan, kananan ‘yan kasuwa za su karbi tallafi daga Naira 100,000 zuwa Naira 500,000 domin bunkasa sana’o’insu.

Manoma 19,068 za su samu kayan aikin noma, wanda ya haɗa da injunan ban ruwa na sola, ‘ya’yan kifi, da kaji, domin inganta harkar noma a jihar. Wannan mataki na nuni da jajircewar gwamnatin jihar wajen tallafawa manoma da inganta aikin gona.

Gwamna Radda ya jaddada cewa an gudanar da tsare-tsaren sa-ido domin tabbatar da cewa an cimma manufar shirin. Wannan tallafi na Naira biliyan 3.9 yana da mahimmanci wajen inganta rayuwar al’umma da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar Katsina.