Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

EFCC Ta Kwato Naira Biliyan 248 Da Dala Miliyan 105 Daga Hannun Barayi

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya (EFCC) ta bayyana nasarorinta a yaƙin da take yi da masu wawushe dukiyoyin jama’a. A cikin sanarwar da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ya fitar, EFCC ta kwato Naira biliyan 248 da Dala miliyan 105 daga hannun barayi.

Daraktan ɓangaren shari’a na ONSA, Zakari Mijinyawa, ya bayyana hakan a wani taron kwamitin tsare-tsare na harkokin sadarwa tsakanin hukumomin gwamnati a Abuja. Ya kuma ce hukumar ta samu nasarori a kan shari’o’in da ta shigar da wadanda ake zargi da laifuffuka, inda har yanzu ana ci gaba da gudanar da shari’o’i guda 3,455.

Hakanan, hukumar ta bayyana cewa tsofaffin gwamnoni huɗu da wasu tsofaffin ministoci suna fuskantar shari’a bisa zargin karkatar da kuɗaɗe da sauran laifuffuka. A cikin yaƙin da ake yi da satar mai, an bayyana cewa sojoji sun daƙile satar man da ya kai Naira biliyan 57.05.

Mijinyawa ya jaddada ƙoƙarin da hukumomi ke yi wajen kare albarkatun man fetur na ƙasar, inda aka yi kira ga kowane dan kasa da ya taimaka wajen gano masu laifi. Wannan nasara ta EFCC na nuna yadda hukumar ke ci gaba da gudanar da ayyuka na musamman don shawo kan cin hanci da rashawa a Najeriya.