ECOWAS Ta Ba Kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso Watanni 6 Don Sake Nazari a Ficewarsu

Kungiyar ECOWAS ta amince da ficewar kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso daga cikin kungiyar, inda aka ba su wa’adin watanni shida daga 29 ga Janairu zuwa 29 ga Yuli, 2025, don sake nazarin matsayinsu na ficewa.

Shugaban hukumar ECOWAS, Omar Touray, ya sanar da wannan wa’adin a ranar Lahadi bayan taron kolin shugabannin kungiyar karo na 66 da aka gudanar a Abuja. Wannan matakin na nufin bai wa kasashen uku damar tunani da sake duba shawarar su na ficewa daga kungiyar.

ECOWAS na fatan cewa kasashen da ke karkashin mulkin soja za su dawo cikin kungiyar, yana mai cewa an kafa kwamitin da zai bibiyi yadda za a gudanar da ficewar kasashen.

Hukumar ta bayyana cewa ficewar kasashen uku daga cikin ECOWAS za ta fara ne daga Janairu, amma wannan karin lokaci na watanni shida zai ba su damar duba al’amuransu kafin a kammala ficewar.

Shugaban hukumar kula da ECOWAS ya bayyana cewa wannan shiri yana da matukar muhimmanci ga alakar siyasa da tattalin arziki tsakanin kungiyar da kasashen da suka fice.