Kotu Ta Ba da Belin N500m ga Yahaya Bello Tare da Kafa Sharudda

Kotun tarayya da ke Abuja ta yanke hukunci kan belin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a cikin wani shari’a da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta shigar. An ba wa Yahaya Bello belin Naira miliyan 500, tare da kafa wasu sharudda masu tsauri.

Mai shari’a Emeka Nwite ya umurci Yahaya Bello da ya mika fasfon sa na kasa da kasa, tare da dakatar da shi daga tafiye-tafiyen waje ba tare da izinin kotu ba. Haka kuma, an umarci masu tsaya masa a kan belin su gabatar da takardun mallakar filaye a Abuja don tantancewa.

Kotun ta bayyana cewa Yahaya Bello zai zauna a kurkukun Kuje har sai ya cika wadannan sharuddan kafin a saki shi. An tsayar da ranakun 24 da 28 ga Fabrairu na shekara mai zuwa domin fara sauraron shari’ar da EFCC ta gabatar kan zargin almundahanar Naira biliyan 80.

Hukumar EFCC ta zargi Yahaya Bello da amfani da wasu mutane wajen siyan kadarori masu tsada a Abuja da Dubai yayin da yake mulki daga 2016 zuwa 2024. Wannan lamari na ci gaba da jan hankalin jama’a game da harkokin cin hanci da rashawa a Najeriya.