NLC Ta Matsa Gwamna Ya Amince da N80,000 a Mafi Ƙarancin Albashi

Gwamnatin jihar Bayelsa ta amince da sabon mafi ƙarancin albashi na N80,000 ga ma’aikatan kananan hukumomi. Wannan matakin ya biyo bayan matsin lamba daga ƙungiyoyin ƴan kwadago, musamman Ƙungiyar Ƴan Kwadago ta Najeriya (NLC) da Ƙungiyar Ƴan Kwadago ta Tarayya (TUC).

Muƙaddashin gwamnan jihar, Lawrence Ewhrudjakpo, ya bayyana hakan ranan talata a lokacin taron kwamitin aiwatar da dokar albashi a gidan gwamnati da ke Yenagoa. Ya ce wannan sabon tsarin zai fara ne a watan Disamba, wanda hakan zai kawo canji mai kyau ga ma’aikatan kananan hukumomi a jihar.

Ewhrudjakpo ya bayyana cewa jihar Bayelsa ba ta da ƙarfin tattalin arziki da zai iya biyan sabbin ƙa’idodin gwamnatin tarayya, amma sun yanke shawarar ƙara albashin ma’aikata don inganta rayuwarsu. Ya ce:

“Mun amince cewa N80,000 ya zama sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikatan kananan hukumomi.”

Bugu da ƙari, gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta yi nazari kan karin kuɗin fansho bisa ga umarnin gwamnatin tarayya. Ya bayyana cewa gwamnatin Douye Diri ta ƙara N10,000 a albashin ma’aikatan da suka yi ritaya, wanda ke nuni da kyakkyawar niyyar gwamnati wajen inganta rayuwar ma’aikata.

A wannan lokaci, amincewar gwamnan ta kasance mai matuƙar muhimmanci ga ma’aikatan jihar, wanda hakan zai taimaka wajen rage talauci da inganta walwala a tsakanin al’umma. Wannan mataki na gwamnatin Bayelsa na nuna alamar cewa suna bin diddigin bukatun ma’aikata da kuma kyautata yanayin aikinsu.