Yan Tawaye Sun Kwace Iko a Syria: Bashar Al Assad Ya Tsere

Ana fargabar cewa yan tawaye sun kwace iko a kasar Syria, yayin da ake tunanin shugaban kasar, Bashar al-Assad, ya tsere daga babban birnin, Damascus. Wannan lamari ya biyo bayan shafe shekaru 13 ana yakin basasa a kasar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa yan tawaye sun ayyana nasarar kwace iko a ranar 7 ga watan Disamba, inda suka bayyana hakan a matsayin “karshen zalunci” a kasar. A wannan lokaci, dubban fursunonin siyasa sun kubuta daga gidajen yari na gwamnati, abin da ke nuni da ƙarshen mulkin Assad.

Kakakin ‘yan tawaye ya bayyana cewa wannan nasara babbar ci gaba ce ga mutanen Syria da suka sha wahala. Hakan na zuwa ne bayan zarge-zargen gwamnatin Assad na take hakkin dan Adam, ciki har da amfani da makaman gas kan fararen hula.

Duk da cewa ba a tabbatar da inda Bashar al-Assad yake ba, wannan yanayi yana bayyana canje-canje masu tarihi a kasar Syria, wanda ke fuskantar matsaloli da yawa tun daga yakin basasa na shekarar 2011.