
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya bayyana cewa jam’iyyar APGA a shirye take ta haɗa kai da wasu jam’iyyun siyasa kafin zaben 2027. Wannan bayani ya fito ne a lokacin taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar APGA a Abuja ranar Juma’a.
Soludo ya jaddada cewa ƙofar APGA a buɗe take ga kowace jam’iyya mai aƙidar ci gaban Najeriya, yana mai cewa jam’iyyar tana son haɗa karfi da karfe domin inganta harkokin siyasa da tattalin arziki a ƙasar.
A cewarsa, “APGA a shirye take ta ƙulla ƙawance da duk jam’iyyar da ke da ra’ayi da akidar ci gaba na gaskiya, domin haɗa kai wajen sake gina Najeriya.” Ya kuma bayyana cewa bayan warware duk wata taƙaddama da jam’iyyar ta fuskanta, APGA na cikin shirin kulla haɗin gwiwa da sauran jam’iyyun da ke son ci gaba.
Gwamnan ya yi nuni da cewa jam’iyyar APGA, wadda aka kafa a hukumance a shekarar 2002, ta kasance mai aƙidar kawo ci gaba a Najeriya. Wannan mataki na APGA na buɗe ƙofar haɗin kai na nufin inganta haɗin gwiwa da sauran jam’iyyun siyasa a ƙasar, musamman a lokacin da ake fuskantar kalubale da dama a fannin siyasa.
Gwamna Soludo ya yi kira ga sauran jam’iyyun siyasa da su hada kai da APGA domin samun nasara a zaben 2027, yana mai jaddada cewa haɗin gwiwa zai taimaka wajen inganta rayuwar al’umma da kuma samun ci gaba mai ɗorewa a Najeriya.