
Jam’iyyar PDP ta sallami ɗan Majalisar Wakilai daga jihar Imo, Hon. Ikenga Imo Ugochinye, bisa zargin rashin ɗa’a da zagon ƙasa. Wannan mataki ya biyo bayan binciken da aka gudanar kan zargin da aka yi masa, wanda aka kammala ranar Alhamis da ta wuce.
Sakataren PDP na jihar Imo, Lancelot Obiak, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, 6 ga watan Disambar 2024. A cewar sanarwar, PDP reshen ƙaramar hukumar Ideato ta kori ɗan majalisar bayan kammala bincike kan zargin da ake masa.
PDP ta bayyana cewa an kori Ikenga Imo Ugochinye ne saboda rashin adabi da kuma cin amanar jam’iyya. A cikin sanarwar, Obiak ya ce shugaban jam’iyyar na Ideato, ThankGod Okeke, da sakataren sa, Onyebuchi Umeh, sun sanya hannu a kan wasiƙar korar da aka tura ga hukumar PDP ta jihar.
Tun farko, PDP ta dakatar da ɗan majalisar daga gundumarsa bayan ya ƙi mutunta gayyatar da aka masa a ranar 14 ga watan Oktoba. A cikin sanarwar, PDP ta bayyana cewa kwamitin zartarwa na PDP a karamar hukumar Ideato ta Arewa ya yi taro ranar 5 ga Disamba, inda suka amince da rahoton kwamitin ladabtarwa.
PDP ta bayyana cewa wannan korar na daga cikin matakan da za su ɗauka na tabbatar da tsaron jam’iyyar da kuma inganta gudanarwar siyasa a jihar. Wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin siyasa, inda ake sa ran ganin yadda zai shafi harkokin jam’iyyar a nan gaba.