
Gwamnatin Najeriya, a karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, ta kulla yarjejeniyar hakar ma’adanai tare da kasar Faransa. Wannan yarjejeniyar ta haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin al’umma, musamman ma ganin yadda wasu kasashe ke yanke alaka da Faransa kan harkokin hakar ma’adanai.
A makon da ya gabata, Tinubu ya kai ziyara Faransa inda aka rattaba hannu kan yarjejeniyar da ke nufin inganta hakar ma’adanai a Najeriya. Wannan matakin na zuwa ne a lokacin da Jamhuriyar Nijar ta tsuke iyakokin hako ma’adanan uranium din ta daga hannun Faransa.
Yarjejeniyar ta kunshi abubuwa masu muhimmanci, ciki har da:
- Hada kai wajen bincike da hakar ma’adanan: Wannan yana nufin cewa Najeriya za ta karbi sabbin fasahohi da dabaru daga Faransa.
- Musayar dalibai: Wannan zai ba da damar horas da matasa a fannin hakar ma’adanai.
- Rage illa ga muhalli: Yarjejeniyar ta tanadi hakar ma’adanai cikin tsafta da bin ka’idoji don kare muhalli.
Ministan ma’adanai, Dr. Oladele Alake, ya bayyana cewa wannan yarjejeniya za ta kara fito da martabar Najeriya a fannin hakar ma’adanai a duniya.
Duk da haka, akwai damuwa daga wasu ‘yan Najeriya game da wannan haɗin gwiwa, musamman ganin cewa Nijar ta yanke alaka da Faransa kan hakar uranium, wanda ya sa Najeriya ta karbi Faransa a fannin hakar ma’adanai. Wannan ya jawo hankalin masu lura da harkokin diplomasiyya, musamman ma a lokacin da akwai rade-radin cewa Faransa na shirin kafa sansanin soji a Najeriya.
Yarjejeniyar ta zo da fata na samar da cigaba a fannin hakar ma’adanai, tare da hasashen samun kudin shiga da za a yi amfani da shi wajen inganta tattalin arzikin Najeriya. Duk da haka, akwai fargabar tsaro da mutane ke nunawa kan zuwan Faransa, tare da wasu masu ra’ayi suna cewa wannan na iya zama sanadiyyar sabbin matsaloli a cikin kasar.
Da karshe, ana sa ran ganin yadda wannan yarjejeniyar za ta tasiri kan harkokin hakar ma’adanai a Najeriya da kuma tasirin da za ta yi ga tattalin arzikin kasar.