
Rundunar tsaro a Najeriya ta yi martani kan jita-jitar da ake yaɗawa cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi yarjejeniya da Faransa kan kawo sojojinta Najeriya. Hafsan tsaron kasar, Janar Christopher Musa, ya musanta labarin da ke cewa an ba Faransa izinin kafa sansanin sojoji a Najeriya, musamman a yankin Arewa.
Janar Musa ya bayyana cewa babu wata ƙungiya ta kasashen waje da za ta iya kafa sansanin sojoji a Najeriya ko a ko’ina cikin ƙasar. Ya ce, “Babu wani abu makamancin haka, shugaban kasa ya fahimci muhimmancin kare ƙasar nan kuma ba zai taɓa bari wata ƙungiyar ƙasashen waje ta kafa sansani a Najeriya ba.”
Wannan martani ya biyo bayan rade-radin da suka bayyana cewa Tinubu ya haɗa baki da Faransa domin kafa sansanin sojoji tare da hadin guiwa kan hakar ma’adinai. Janar Musa ya tabbatar da cewa duk wani abu da Shugaban ƙasa ya sanya hannu a kai, yana da alaƙa da yarjejeniyar hadin guiwa kan cinikayya, al’adu, da tattalin arziki.
Wannan al’amari na jawo hankalin al’umma da dama, wanda ke nuna yadda alakar Najeriya da Faransa ke fuskantar tantanin ra’ayi tsakanin mambobin al’umma da shugabanni. Al’ummar Najeriya na sa ran karin bayani daga gwamnatin tarayya kan wannan batu, wanda ke da matuƙar muhimmanci ga tsaron ƙasar.