Tsohon Dan Takarar Gwamna da Magoya Bayansa Sun Fice daga Jam’iyyar LP

Tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar LP a jihar Edo, Kenneth Imansuangbon, ya fice daga jam’iyyar tare da magoya bayansa. Wannan matakin na Imansuangbon ya kasance ne a cikin wani takarda da ya aikewa shugaban jam’iyyar LP na ƙasa, Julius Abure, da kuma shugaban jam’iyyar a gundumarsa ta Ewohimi.

Imansuangbon ya bayyana cewa rigingimin cikin gida da rashin tsari a jam’iyyar su ne dalilan da suka sa ya yanke shawarar ficewa. Ya zargi shugabannin LP da cewa sun maida jam’iyyar tamkar dandalin kasuwanci, wanda hakan ya sa ta gaza zama zaɓin da ‘yan Nijeriya ke so. A cewarsa, “Jam’iyyar LP ta kauce daga kan turbar da aka kafa ta a kai.”

Tsohon dan takarar ya sha kaye a zaben fitar da ɗan takarar gwamna a hannun tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi, Olumide Akpata, kuma a cikin zaben gwamnan jihar Edo da aka yi a ranar 16 ga watan Nuwamba, LP ta samu matsayi na uku a yawan ƙuri’u.

Imansuangbon, wanda aka san shi da suna “Mutumin shinkafa” saboda rabon shinkafa kyauta da yake yi a duk shekara a jihar Edo, ya ce bayan tuntubar magoya bayansa a fadin jihar, ya ga ya zama dole su fice daga jam’iyyar LP.

A baya, Imansuangbon ya kasance cikin jam’iyyun APC da PDP, yana mai cewa wannan mataki na ficewa yana da nasaba da burin sa na ci gaba da kawo canji a jihar Edo.