Malamin Musulunci Ya Fadi Abin da Ake Tunkara a Najeriya da Ya Fi Kudirin Haraji Masifa


Yayin da ake ta tattaunawa kan sabon kudirin haraji a Najeriya, Sheikh Murtala Bello Asada ya bayyana cewa akwai wata masifa da ake tunkara wacce ta fi wannan haraji masifa. Malamin ya nuna damuwa game da alakar Shugaba Bola Tinubu da kasar Faransa, yana mai cewa wannan alaka na iya jawo fitina musamman a jihar Sokoto.

Sheikh Bello Asada ya yi wannan furuci a cikin wani faifan bidiyo da shafin Karatuttukan Malaman Sunnah ya wallafa a Facebook. Ya jaddada cewa ana mayar da hankali kan kudirin haraji, alhali akwai wasu matsaloli masu girma da suka shafi tsaron kasa da kuma hadin gwiwa da sojojin Faransa.

Malamin ya ce, “Ya ku al’ummar Musulmi, hadarin da muke fuskanta an juyar da hankalin mutane kan maganar haraji. Akwai bala’in da ya fi na haraji, Bola Tinubu ya zo ya hada kai da Faransa domin kawo sojoji Najeriya a tono ma’adinai.”

Sheikh Asada ya kuma goyi bayan Nijar, yana mai cewa duk wanda zai yaki Nijar to da su zai yi fada domin su mara mata baya dari bisa dari. Ya yi addu’ar cewa Allah ya kawo mana saukin wannan zalunci da muke fuskanta.

Wannan jawabi ya jawo hankalin jama’a kan cewa akwai bukatar a mai da hankali kan abubuwan da ke faruwa a kasa fiye da kudirin haraji kawai.