Kudirin Sauya Fasalin Harajin Tinubu Ya Ƙara Gamuwa da Cikas a Jihar Kano


Kudirin sauya fasalin harajin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar a majalisar tarayya ya gamu da cikas a jihar Kano. Majalisar dokokin jihar Kano ta yi fatali da kudirin a zamanta na ranar Litinin, 2 ga watan Disamba, 2024, karkashin jagorancin kakakin majalisa, Rt. Hon. Ismail Falgore.

Majalisar ta roƙi sanatoci da ƴan majalisar wakilai na Arewa su yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa kudirin bai tsallake ba. Shugaban masu rinjaye na majalisar, Lawan Husseini, ya gabatar da kudirin gaggawa kan batun sauya fasalin harajin, inda ya bayyana cewa idan kudirin ya zama doka, zai iya jefa yankin Arewa cikin matsala.


Husseini ya bayyana cewa wannan kudiri yana nufin zagon kasa ga tattalin arzikin Arewa, yana mai cewa:

“Muna kallon kudirin a matsayin wani shiri da aka tsara da nufin zagon kasa ga tattalin arziki da ma kara wahalhalu da kuma talauta yankin Arewa gaba daya.”

Ya kuma jaddada cewa tsarin kasafta harajin VAT da ke cikin kudirin zai shafi jihohi masu karancin kudaden shiga, yayin da wasu jihohin kamar Legas za su ci gajiyar wannan tsarin.

Majalisar dokokin Kano ta ba ƴan majalisar Arewa shawara su haɗa kai don tabbatar da cewa kudirin bai zama doka ba. Wannan mataki na nuna yadda majalisar ke son kare muradun al’ummar Arewa a cikin wannan tsarin haraji.
A halin yanzu, al’umma na jiran matakan da za a dauka daga ƴan majalisar tarayya na Arewa kan wannan batu.