Jonathan Ya Ware Gwamna 1 a Najeriya, Ya Kira Shi ‘Janar’ a Siyasa



Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya samu yabo daga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, wanda ya kira shi ‘Janar’ a siyasa. Jonathan ya bayyana Gwamna Fubara a matsayin mai jajircewa wajen tabbatar da ci gaba a jihar Rivers da yankin Neja Delta.

Jonathan ya yi wannan jawabi ne a yayin taron nadin sarautar gargajiya, inda ya jaddada cewa babu wanda zai zama Janar ba tare da fafatawa a yaki ba. Ya yabawa Fubara kan jarumtarsa da goyon bayan al’umma, yana mai cewa:

“Duk kalubale da kake fuskanta suna gina ka ne saboda gobe.”

Tsohon shugaban kasar ya roƙi al’ummar jihar Rivers da su ci gaba da ba Gwamna Fubara goyon baya don ci gaban yankin Neja Delta. Jonathan ya bayyana cewa zaman lafiya a jihar yana da matukar tasiri ga ci gaban yankin da tattalin arzikin Najeria

Har ila yau, Jonathan ya koka kan rashin haɗin kai a Najeriya, yana mai cewa ci gaba ba zai samu ba idan ba a shawo matsalar haɗin kai ba. Ya bayyana damuwa kan cewa har yanzu ana fama da rashin haɗin kai bayan shekaru sama da 100 da haɗewar ƙasar.

Wannan yabo daga tsohon shugaban kasa na nuna irin rawar da Gwamna Fubara ke takawa a siyasar jihar Rivers da kuma fatan samun ci gaba mai dorewa a yankin Neja Delta.