Wednesday, April 22Labarai Masu Muhimmanci

Gwamna Radda Ya Amince da Mafi Karancin Albashi, Ya Fadi Abin da Zai Biya Ma’aikata

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda, ya sanar da sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata a jihar. An amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi bayan an kammala tattaunawa kan wannan batu.

A cikin sanarwa da ya fitar, Gwamna Radda ya bayyana cewa za a fara biyan sabon tsarin albashin daga watan Disamba na shekarar 2024. Wannan sabon tsarin albashi zai shafi ma’aikata a dukkan ɓangarorin gwamnati, ciki har da jihohi, ƙananan hukumomi, da hukumar kula da ilimi ta ƙananan hukumomi.

Gwamnan ya nuna godiya ga ma’aikatan jihar bisa haƙurin da suka nuna a lokacin tattaunawar. Ya ce, “Barkanmu da safiya Katsinawa, bayan tattaunawa mai inganci, ina mai farin cikin sanar da amincewa da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.”

Wannan mataki na gwamnan na nuni da kokarin inganta rayuwar ma’aikata a jihar Katsina, tare da fatan ganin karin jin dadin ma’aikata da ingancin aikin gwamnati a jihar.