Gwamnan Kano Ya Cika Alkawari: Ma’aikata Sun Fara Cin Sabon Albashin N71,000

Gwamnatin jihar Kano ta fara biyan ma’aikata sabon mafi karancin albashi na N71,000, wanda gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin aiwatarwa. Wannan sabuwar dokar albashi ta fara aiki ne a watan Nuwamba, 2024, bayan karɓar rahoton kwamitin da aka kafa don tantance sabon albashin.

Shugaban ma’aikatan jihar, Alhaji Abdullahi Musa, ya tabbatar da fara biyan sabon albashin a ranar 25 ga watan Nuwamba, yana mai jaddada cewa wannan karin albashi na da matukar mahimmanci ga ma’aikata. Ya roki ma’aikatan su yi amfani da karin albashin cikin hikima da tsoron Allah, domin inganta rayuwarsu.

Alhaji Abdullahi Musa ya bayyana cewa, “Tun ranar da mai girma gwamna ya sanar da sabon mafi ƙarancin albashin nan, na san cewa za a gani a aikace.” Ya kuma nuna godiya ga gwamnan bisa cika alkawarin da ya yi.

Gwamnatin jihar ta kuma fara biyan alawus-alawus ga ma’aikatan lafiya, wani mataki da ke nufin inganta jin dadin ma’aikata a fannin kiwon lafiya. Wannan sabuwar dokar albashi na nufin rage radadin talauci da ma’aikata ke fuskanta, tare da jaddada muhimmancin aiki tukuru da tsoron Allah a dukkan ayyukan da za su yi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin ci gaba da inganta rayuwar ma’aikata da talakawa a jihar, tare da tabbatar da cewa an aiwatar da dukkan shirin da aka tsara don inganta ilimi da jin dadin al’umma.