
Daga babban birnin Tarayya Abuja: Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa (EFCC) ta kama tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a ranar 26 ga watan Nuwamba, 2024, a hedkwatar hukumar da ke Abuja. Wannan mataki na hukumar ya biyo bayan zarginsa da aikata laifuka da suka shafi cin hanci da rashawa.
Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da kama Yahaya Bello ga manema labarai, inda ya ce dakarun hukumar ne suka gudanar da aikin. Oyewale ya bayyana cewa, “Eh gaskiya ne, muna tsare da shi a hannun mu yanzu haka.”
Yahaya Bello, wanda ya kasance gwamnan jihar Kogi, ya tura tawagar lauyoyi zuwa ofishin EFCC domin amsa gayatar da aka masa. An zarge shi da karkatar da kuɗaɗen jama’a har naira biliyan 80.2. Wannan lamari ya jawo hankalin jama’a da dama, tare da sa suyi ta zantawa kan yadda hukumomin Najeriya ke gudanar da bincike kan manyan mutanen da ake zargi da cin hanci.
Bayan tsawon lokaci yana ɓuya, Yahaya Bello ya bayyana a hedkwatar EFCC, inda ya nuna sha’awarsa na kare kansa daga zargin da ake masa. A halin yanzu, ana gudanar da bincike kan tsohon gwamnan a cikin ofishin hukumar.
Kama Yahaya Bello na daga cikin matakan da hukumar EFCC ke ɗauka wajen yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya. Wannan lamari na jawo hankalin mutane da dama, yana mai nuni da yadda hukumomi ke aiki domin tabbatar da adalci a cikin al’umma. Za a ci gaba da bibiyar wannan lamari domin samun karin bayani a nan gaba.