
Ƴar majalisar wakilai, Hon. Erhiatake Ibori-Suenu, ta bayyana dalilinta na sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC, inda ta ce matakin da ta ɗauka yana kan doka. Ibori-Suenu, ɗiyar tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori, ta yi wannan bayani ne a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda ta ƙalubalanci matakin PDP na ayyana kujerarta da babu kowa.
A cikin takardar ƙorafin da ta shigar a kotu, Ibori-Suenu ta ce, “Ban saɓawa tanadin kundin tsarin mulki ba,” tana mai jaddada cewa sauya shekar da ta yi bai sabawa kowanne doka ba. Ta bayyana cewa wannan mataki na komawa APC yana da inganci, kuma PDP ba ta da hakkin ayyana kujerarta a matsayin babu kowa.
Ibori-Suenu ta sanar da komawarta APC a hukumance a zauren majalisar a ranar Alhamis, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar adawa. A cewarta, rigingimun cikin gida da PDP ke fama da su sun jawo mata rashin jin daɗi, wanda hakan ya tilasta ta dauki wannan mataki.
Hon. Ibori-Suenu ta lashe zaben wakili a mazaɓarta ta Ethiope ta Gabas/Yamma a zaben 2023, a lokacin da ta yi takara a inuwar jam’iyyar PDP, duk da saɓanin siyasa da gwamnan jihar Delta mai ci, Ifeanyi Okowa, ke fuskanta da mahaifinta. PDP ta yi fatali da sauya shekar Ibori-Suenu, inda ta bayyana cewa ta rasa kujerarta tun lokacin da ta zabi komawa APC.
A cikin takardar da ta shigar a kotu, Ibori-Suenu ta sanya shugaban majalisar, magatakarda, da jam’iyyar PDP a matsayin wanda take ƙara. Ta bayyana cewa, “Sama da shekara guda PDP na fama da rigingimu wanda har ta kai ga jam’iyyar ta dare gida biyu.”
Wannan sauya sheƙar na Ibori-Suenu yana daga cikin jerin canje-canje da ‘yan majalisar ke yi a tsakanin jam’iyyun siyasa a Najeriya, inda wasu ‘yan majalisa ke kokarin karfafa matsayin su a cikin sabbin jam’iyyun da suka shiga. Hakan na nuna yadda siyasar Najeriya ke canzawa da sauri, tare da jawo hankalin masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa.