Wednesday, April 30Labarai Masu Muhimmanci

Ƴan Kwadago Sun Fara Neman Ƙarin Albashi a 2025 Saboda Tsadar Rayuwa

Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta TUC, Festus Osifo, ya bayyana cewa ƴan kwadago a Najeriya sun fara fafutukar neman ƙarin albashi fiye da N70,000 a shekara mai zuwa. Wannan mataki na zuwa ne a matsayin martani ga hauhawar farashin kayayyaki da ke shafar rayuwar ma’aikata a ƙasar.

Osifo ya bayyana a shirin siyasa na Channels TV cewa ya kamata gwamnati ta dinga kimanta mafi ƙarancin albashin ma’aikata bisa la’akari da farashin kayayyaki a duk shekara, maimakon jira shekaru biyar kafin a yi wani gyara. Ya ce: “Maimakon mu jira shekaru biyar kafin ƙarin mafi ƙarancin albashi, me zai Hana a yi shi yanzu? Ya kamata a dinga yi wa ma’aikata ƙarin albashi duk shekara.”

Shugaban ƙungiyar kwadago ya ce tattaunawar kan ƙarin albashi ta riga ta fara, tare da haɗin gwiwar ƙungiyar NLC. A cewarsa, idan hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta fitar da alkaluman hauhawar farashin kaya, wannan zai taimaka wajen tantance ko ya dace a yi ƙarin albashi.

Osifo ya bayar da misali cewa idan hauhawar farashin kaya ya kai kashi 35%, to ya kamata a yi amfani da wannan adadi don sabunta mafi ƙarancin albashi na N70,000. Wannan yana nuni da yadda ƴan kwadago ke son a dinga sabunta albashi daidai da yanayin kasuwa.

A cikin watan Yulin 2024, bayan tsawon watanni ana tattaunawa, gwamnatin tarayya da ƴan kwadago sun cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000. Wannan sabon tsarin albashi na da matuƙar tasiri ga walwalar ma’aikata, amma tare da ci gaban hauhawar farashi, akwai bukatar a ci gaba da duba wannan lamari.

Osifo ya jaddada cewa ƴan kwadago na son a mai da hankali kan inganta walwalar al’umma a 2025, tare da neman gwamnati ta dinga bayar da kulawa ga halin da ma’aikata ke ciki. Wannan mataki na nuna cewa ƴan kwadago suna tare da al’umma wajen ganin an inganta rayuwar su da ta sauran al’umma.