
An saki ma’aikatan binciken ƙasa guda tara da aka sace a jihar Ondo bayan an biya ƴan bindiga kudin fansa na Naira miliyan 20. Wannan lamarin ya faru ne bayan sun kwashe sama da mako guda a hannun masu garkuwa da mutane.
Rahotanni sun bayyana cewa ma’aikatan sun tsira daga hannun ƴan bindigar ne a daren Talata, bayan da aka karɓi kudin fansa. Ƴan bindigar sun nemi a biya su Naira miliyan 100 kafin su sako su, wanda ya jefa dangi da abokan aiki cikin damuwa.
Wani daga cikin ‘yan uwan waɗanda aka sace, Fasto Ajibade Owolanke, ya tabbatar da cewa an sako su ne bayan an biya ƴan bindigar Naira miliyan 20. Ya bayyana cewa wasu daga cikinsu sun riga sun koma gida, yayin da wasu ke asibiti ana kula da lafiyarsu.
A cewarsa, waɗanda aka sace sun fuskanci azaba mai tsanani da wahala a hannun ƴan bindigar. Wannan lamari ya jawo hankalin jama’a, inda mata ‘yan kasuwa daga yankin suka gudanar da zanga-zanga a ofishin Gwamna Lucky Aiyedatiwa, suna neman gwamnati ta dauki mataki kan karuwar hare-haren garkuwa da mutane.
Har yanzu, babu wata sanarwa daga rundunar ‘yan sanda ta jihar Ondo kan wannan ci gaban, wanda ke kara tayar da hankalin al’umma. Jama’a sun yi kira ga hukumomi da su gaggauta daukar matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma daga hare-haren ƴan bindiga.