Ƴan Bindiga Sun Koma Garin Ofoloke, Sun Kashe Matasan Sa-Kai

A ranar Asabar, 18 ga watan Mayu, 2025, Ƴan bindiga sun kai hari a garin Ofoloke, jihar Kogi, inda suka hallaka matasa uku da ake zargin su na aikin sa-kai. Wannan lamari ya biyo bayan sace sarkin garin, HRM Ogunyanda Ilufemiloye, daga cikin fadarsa a ranar Alhamis da ta gabata.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa matasan suna kokarin kare ma’aikatan da suka je gyara na’urorin sadarwa a daji lokacin da wannan mummunan hari ya faru. Wani dan yankin, Demola Samuel, ya bayyana cewa al’umma na cikin fargaba, yana mai cewa: “Dole ne a dauki matakan tsaro, mutane na barin yankin saboda tsoron abin da zai biyo baya.”

Wannan hari na Ƴan bindiga ya jawo hankalin hukumomi da al’ummar yankin, wanda ya nuna cewa akwai bukatar gaggawa wajen inganta tsaro a jihar. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, SP William Aya, bai amsa kiran waya da aka yi masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Halin da sarkin ke ciki har yanzu ba a bayyana ba, yayin da al’umma ke fuskantar fargaba da tsoro sakamakon wannan tashin hankali. Al’ummar Ofoloke na fatan samun kariya daga hukumomi don dakile wannan mummunan lamari na kisan kai.