Ɗan Hayar Kisan Kai da Bindiga a Hannun Ƴan Sanda a Gombe

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta yi nasarar kama wani matashi ɗauke da bindiga da harsasai, wanda ake zargin an ɗauke shi hayar kisa a jihar Filato.

An kama Joseph Babari ne a wani binciken tsaro da ‘yan sanda suka gudanar a kan hanyar jihar Gombe. Yana ɗauke da bindiga kirar gida, harsasai takwas, rigar yaki da kuma kayan tsafi.

Binciken farko ya nuna cewa an ɗauki Babari hayar ne domin ya je ya yi faɗa a wani yankin da rikici ya addaba a jihar Filato, akan kuɗi N180,000 na tsawon wata biyu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce za su ci gaba da bincike domin gano daga ina makamin ya fito da kuma wa ya ɗauki matashin aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *