Ƙungiyar ‘Obidient’ Ta Ce Wa APC: Ba Za Ku Iya Lashe Zaɓe Mai Gaskiya A Najeriya Ba

Ƙungiyar ‘Obidient’ a Jihar Delta ta bayyana cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba za ta iya lashe ko wane irin zaɓe mai gaskiya a Najeriya ba, saboda ƙarancin ayyukan da jam’iyyar ta yi a ƙasa da kuma ƙaruwar rashin jin daɗin jama’a.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai da aka gudanar a karshen mako a Asaba, Shugaban Majalisar Dattawa na ‘Obidients’ a Delta, Cif Chris Boise, ya yi watsi da sauya shekar da wasu mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) suka yi zuwa APC a jihar, yana mai cewa matakin ba zai shafi siyasar Delta ba.

Ya ce: “Ba mu damu ko kaɗan game da haɗewar ‘yan PDP zuwa APC. Dalilinsu na cewa wannan sauya shekar zai haifar da ci gaba ba shi da tushe idan aka yi la’akari da mummunan mulkin APC a matakin ƙasa a cikin shekaru goma da suka gabata.”

Boise ya yi nuni da zaɓen shugaban ƙasa na 2023 don ƙarfafa batunsa, yana mai cewa ɗan takarar jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya samu gagarumin rinjaye a Jihar Delta, inda ya lashe ƙuri’u 341,866 idan aka kwatanta da Atiku Abubakar 161,600 da Bola Tinubu 90,183.

Ya zargi gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin APC da jefa Najeriya cikin durƙushewar tattalin arziƙi da ƙara ta’azzara rashin tsaro, yana mai cewa gwamnatin yanzu ba ta dogara da aiki ko goyon bayan jama’a ba, sai dai “ƙaramin masu hannu da shuni” da ke da niyyar ƙarfafa mulki.

Ya ce: “Tun lokacin da APC ta karɓi mulki a watan Mayu 2015, ƙasar ta fuskanci hauhawar rashin tsaro, musamman daga makiyaya Fulani ɗauke da makamai, waɗanda ayyukansu suka lalata al’ummomin manoma a faɗin Najeriya.”

Cif Boise ya bukaci Gwamna Sheriff Oborevwori da ya ɗauki matakai na gaggawa don ƙarfafa tsaro a yankunan ta hanyar baiwa masu gadin gari damar kare ‘yan ƙasa daga hare-haren da mahara ɗauke da makamai ke kaiwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *